Sojojin ruwa na Najeriya sun yi nasarar kama wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a fasa bututan mai a yankin Niger Delta mai arzikin mai.
Wani jami'in sojan ruwa a yankin Rear Admiral Muhammed Garba ya bayyana cewa, an kama mutanen da ake zargin ne a kusa da yankin Batan a cikin makon da ya gabata.
Garba ya kuma shaida wa manema labarai a sansasin sojojin ruwan da ke garin Warri cewa, daga cikin abubuwan da aka samu a wajen mutanen da aka kaman sun hada da kwale-kwale 7 da tan 490 na taceccen man disel.
Ya kuma bayyana cewa, ana yiwa mutane biyar tambayoyi game da zargin da ake musu na hannu a fasa na'urorin kamfanin samar da mai na kasar.
Ana kuma zargin daya daga cikin mutanen da hannu a kisan sojoji 2 a ranar 10 ga watan Mayu a yanikin Batan, yayin da ake zargin gudan da kartar kudi daga hannun jama'a
Kuma da zarar an kammala binciken, za mika su ga hannun hukumomin da suka dace.(Ibrahim)