in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Malawi ya yaba taimakon da Sin ta baiwa kasarsa
2015-06-15 09:57:38 cri

Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ya yaba da irin gudummawar da gwamnati da 'yan kasuwar kasar Sin suka bayar wajen inganta harkokin lafiya da ilimi a kasarsa.

Shugaba Mutharika ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira a gun taron kolin kungiyar kasashen Afirka da ke gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Ya kara da cewa, Sinawa sun dade suna zuba jari a ayyukan tsaftace muhalli a kasar, baya ga kamfanonin kasar ta Sin da su ma ake damawa da su a harkokin kasuwancin kasar.

Shugaba ya ce, ko da a watan Oktoban shekarar da ta gabata, kasar Sin ta baiwa gwamnatinsa rancen dala miliyan 25 don gudanar da wasu ayyukan inganta rayuwar jama'a, musamman gina makarantu.

Bugu da kari, kasar Sin ta taimakawa kasar ta Malawi da rancen dala miliyan 80 wajen kafa jami'ar kimiyya da fasahar kere-kere ta Malawi, wadda ta fara aiki tun a shekarar 2014.

Shugaban na Malawi ya ce, ilimi ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen yiwa yara mata kanana aure, kuma abokan hulda kamar Sin za su ba da gudummawa wajen inganta harkokin ilimi a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China