Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi bayani game da kalaman shugaban Amurka kan batun tekun Nanhai
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta mayar da martani game da kalaman da shugaba Obama na kasar Amurka ya yi kan batun tekun Nanhai a yayin da yake ziyara a kasar Vietnam cewa, kamata ya yi kasashen waje su girmama kokarin da kasashen da ke yankin tekun Nanhai suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankinsu, kuma bai kamata su keta dokokin yankuna da kawo illa ga kiyaye zaman lafiya a yankin ba. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku