Yang Yujun ya bayyana hakan ne jiya Laraba, yana mai cewa jirgin ruwan yaki samfurin Lawrence ya yi kutse a yankin takun tsibiran na Nanhai na kasar Sin ba tare da samun izini daga kasar Sin ba. Kana sojojin kasar Sin sun dauki mataki kan hakan ba tare da bata lokaci ba.
Yang Yujun ya bayyana cewa, shigar jirgin ruwan yakin na Amurka yankin tekun Nanhai na kasar Sin, ba zai canja matsayin mallakar wannan yanki na kasar Sin ba. Ya ce tsokanar da Amurka ta yi ba ta da wani tasiri. Har ila yau a cewar Mr. Yang, Sin za ta ci gaba da aikin sintiri a yankin tekun, da sararin sama bisa bukatu. Za kuma ta kara inganta karfin kiyaye tsaro, da tabbatar da ikon mallakar yankunan ta, tare da kuma kiyaye zaman lafiya da tsaro a yankin tekun Nanhai na kasar. (Zainab)