in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe na hadin gwiwa da Sin domin rage karancin makamashi
2015-09-22 10:37:37 cri

Kasar Zimbabwe na ba da muhimmanci ga dangantakarta ta makamashi tare da kasar Sin domin magance matsalar karancin makamashi dake janyo jinkiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar, in ji ministan kudin kasar Zimbabwe, Patrick Chinamasa a ranar Litinin.

Ministan ya yi wadannan kalamai a yayin wani zaman taro tare da shugaban kamfanin Sinosure Wang Yi wanda ke ziyarar aiki ta kwanaki biyar a karon farko a wannan kasa dake kudancin Afrika.

Kasar Zimbabwe na fama da karancin wutar lantarki mai tsanani dalilin kayayyakin aiki da suka tsufa, kuma suke samar a yanzu haka da rabin kashi na bukatun makamashin kasar na megawatt dubu biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China