in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta nuna takaici game da harin ta'addancin da aka kai a Urumqi na Sin
2014-05-23 13:13:33 cri

Kasar Amurka ta yi allah wadai da mummunan harin ta'addancin da aka kai Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang na kabilar Ugyur, mai cin gashin kanta ta kasar Sin.

A cikin wata sanarwa, kakakin fadar White House, Jay Carney ya ce, wannan wani mugun hari ne mai ta da hankali da aka aiwatar a kan fararen hula, kuma Amurka na adawa da daukacin siffofi na ta'addanci.

Carney ya ce, Amurka na sane da rahotanni, dake nuna cewar, harin ya haddasa asarar rayuka 'yan kasa kimanin 31, a inda kuma wasu adadin mutane 90, suka samu raunuka.

Kakakin fadar ta White House, ya ce, Amurka na mika gaisuwa da jimaminta ga wadanda harin ya rutsa da su da iyalansu, da kuma duk wanda wannan harin ya shafa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China