A kasar Chadi, a kalla kusan kananan 'yan mata biyu bisa uku ne ake ma auren dole kafin su kai shekarun aure. A karkashin yunkurin shugaban kasa da matarsa, hukumomin gwamnati da kungiyoyin fararen hula sun dauki niyyar kawo karshen wannan matsala a cikin shekaru biyar masu zuwa, musammun ma da ta yi kanta cikin al'adun jama'a dake kuma janyo illoli da dama.
Muna cikin wani muhimmin lokaci na tarihin 'yancin dan adam, musammun ma 'yancin yara kanana a cikin kasarmu. Abu ne da ba za mu yarda da shi ba a wannan lokaci, a ci gaba da tilastawa yara kananan auren dole, in ji shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno a yayin da yake kaddamar da kamfen yaki da auren yara kanana.
Serge Constant Bounda, wakilin asusun kula na kananan yara na MDD (UNFPA) a kungiyar tarayyar Afrika, wanda je birnin Addis Abeba domin wannan al'amarin, ya bayyana fatan ganin shirya wani taron kara wa juna sani na shiyyar wanda zai taimaka wajen tallafawa kasashen Afrika kafa wani jadawalin aiki na tarayyar Afrika, domin shiga gaba da bullo da matakan da suka dace domin kawo karshen auratar da kananan yara a nahiyar Afrika. (Maman Ada)