in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da Jose Mario Vaz a matsayin shugaban Guinea-Bissau
2014-06-24 09:45:10 cri

A ranar Litinin ne aka rantsar da mista Jose Mario Vaz a matsayin shugaban kasar Guinea-Bissau bisa wa'adin shekaru biyu masu zuwa, bayan da ya yi rantsuwar kama aiki a gaban shugaban babbar kotun kasar Paulo Santa a yayin wani babban bikin da ya samu halartar mutane fiye da dubu ashirin, da kuma shugabannin kasashen shiyyar guda goma. Daga cikin wadannan shugabanni, akwai shugaban kasar Senegal Macky Sall, Goodluck Jonathan na Najeriya, Alpha Conde na Guinea-Conakry, Blaise Compaore na Burkina-Faso, Yahya Jammeh na Gambiya, Abdoubacar Keita na Mali, Jorge Carlos Fonseca na Cap-Vert, Mahamadou Issoufou na Nijar, John Mahama na Ghana da kuma Boni Yayi na kasar Benin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China