in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabon firaministan Guinea-Bissau
2014-07-04 10:30:45 cri

Sabon firaminstan kasar Guinea-Bissau, Domingos Simoes Pereira da aka nada a ranar 25 ga watan Juni bisa wani kudurin fadar shugaban kasa, ya yi rantsuwar kama aiki a yayin wani bikin da shugaban kasar Guinea-Bissau Jose Mario Vaz ya jagoranta.

Bikin ya gudana a fadar shugaban kasa a gaban idon jakadun kasashen waje dake kasar, wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da kuma shugabannin sojoji, in ji wani 'dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake wurin.

Ina taya murna ga sabon firaminista wanda kuma nake jaddada masa goyon bayana wajen ganin ya fitar wani jadawalin aikin gwamnatinsa, in ji Jose Mario Vaz. Matsalar kasar na bukatar wani aikin gaggawa daga wajen gwamnati, in ji shugaban kasar tare da gayyatar sabon firaministan da ya gabatar cikin gajeren lokaci da mambobin gwamnatinsa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China