Babban bankin Najeriya CBN ya gargadi 'yan kasar game da kashe kudaden kasashen waje a cikin kasar, yana mai cewa, wanda duk aka kama yana aikata hakan na iya fuskantar daurin watanni 6.
Wata sanarwa da ofishin darakta mai kula da harkokin sadarwa na bankin Ibrahim Muazu ya fitar, ta bayyana damuwar CBN game da yadda ake samun karuwar hada-hadar cinikayya, da musaya da kudaden wajen, musamman ma dalar Amurka a cikin kasar. Aikata hakan, a cewar sanarwar, ya saba da tanajin dokar bankin ta shekarar 2007.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, dokar da ta haramta kashe kudaden waje a cikin kasar ta shafi daukacin 'yan kasar, da ma baki, wadanda sau da dama 'yan kasuwa ke karfafa musu gwiwar kashe kudaden na waje.
Daga nan sai sanarwar ta bukaci al'umma da su sanar da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon-kasa wato EFCC, ko bankin na CBN, da zarar sun ga wani ya karya wannan doka. (Saminu)