Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun afkawa babban jami'in soja mai rike da runduna ta 7 na sojan kasar Birgediya Janar Victor Ezugwu a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar sojan kasar kanal Sani Usman, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya aikawa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, sanarwar ta ce, an yi wa jami'in kwanton bauna ne a ranar Talata da misalin karfe 8:30 na safe a lokacin da yake kan hanyarsa ta ziyartar wasu daga cikin sansanonin sojan kasar dake yankin karamar hukumar Bama.
Usman ya ce, soja guda ya rasa ransa, sannan wasu sojojin biyu sun jikkata a lokacin da ake bata kashi tsakanin su da maharani, sai dai rundunar ta ce, ta hallaka mayaka na Boko Haram da dama a yayin artabun, sannan sun yi nasarar kwace mota kirar Toyota Hilux da wasu makamai daga hannun maharani.
Mai magana da yawun rundunar sojan ya ce, wannan arangama ba ta hana jami'in sojan ci gaba da ziyarar tasa ba, sai dai an tafi da gawar soja guda da wadanda suka jikkatan zuwa asibitin Maiduguri.
Usman ya jaddada cewa, rundunar sojan Najeriya ta lashi takobin kawo karshen mayakan Boko Haram daga yankin baki daya.(Ahmad Fagam)