in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana tattaunawa kan batun kundin tsarin mulki a Cote d'Ivoire
2016-06-08 10:35:21 cri

Batun kundin tsarin mulki shi ne ya fi mamaye tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa a kasar Cote d'Ivoire, da aka fara a ranar Talata a birnin Abidjan.

Wannan mataki zai taimaka wajen kara kawo nazari da yin la'akari da shawarwarin kowa da kowa, ta yadda za a cimma wata yarjejeniya daga bangarorin biyu, kan wajabcin bullo da wani kundin tsarin mulki na jamhuriyya ta uku, in ji shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara a lokacin bude taron.

Daga bayan, za a ci gaba da yin shawarwari tare da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da kungiyoyin fararen hula.

Shugaba Ouattara ya jaddada cewa, bayan wadannan haduwa, masu sanya ido kan al'amura za su mikawa kwamitin kwararru shawarwarinsu, sannan a kai su gaban taron ministocin domin yin nazari. Bayan da taron minisocin ya amince da kundin, sannan a isar da shi a gaban majalisar dokoki.

Alassane Ouattara ya sanar da cewa, za'a shirya zaben raba gardama da zabukan 'yan majalisu a lokaci daban daban.

Muna fatan shirya zaben raba gardama a tsakanin watan Satumba da Oktoba, kana kuma zabukan 'yan majalisu a tsakanin watan Nuwamba da Disamba, in ji shugaban kasar.

Gwamnati da 'yan adawa dai sun sha ganawa da juna sau da dama, musammun ma domin tattauna muhimman batutuwa dake shafar fannonin siyasa, tattalin arziki da jama'a da sauransu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China