in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta fara shirin bullo da sabon kundin tsarin mulki
2016-06-02 10:31:39 cri

Shirin bullo da wani sabon kundin tsarin mulki na kasar Cote d'Ivoire ya fara a ranar Laraba, kuma shugaban kasar Alassane Ouattara ya kafa wani kwamitin kwararru domin aikin, a cewar wata majiya mai tushe.

A cewar wata sanarwar fadar shugaban kasa da aka turawa kafofin watsa labaru, wadannan kwararru guda goma za a dora masu nauyin shirya shawarawarin dake da nasaba da kundin tsarin mulki.

Ta wani bangare kuma, shugaban kasa yana shirin yin tattaunawa tare da 'yan adawar siyasa, shugabannin al'ummomi da kungiyoyin fararen hula wadanda su ma ake tsimin taimakonsu.

Rubuta wani sabon kundin tsarin mulki ya kasance daya daga cikin alkawuran da shugaba Alassane Ouattara ya dauka a lokacin yakin neman zabe, da aka sake zabe a cikin watan Oktoban da ya gabata bisa wani wa'adin mulki na biyu.

Ya kamata a samu wani sabon kundin tsarin mulki da zai tabbatar da daidaici ga kowa, hadin kan kasa da dorewar hukumominmu, in ji shugaba Ouattara.

Za'a gudanar da zaben raba gardama domin baiwa 'yan kasar Cote d'Ivoire damar bayyana ra'ayinsu kan tushen wani sabon kundin tsarin mulki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China