in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar yammacin Afrika na taro a Abidjan kan yaduwar kananan makamai
2016-04-20 10:36:29 cri

Wani taron da ya tattara kwamitocin kasashe na yaki da yaduwar kananan makamai a kasashen yammacin Afrika na gudana a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, da zummar karfafa sanya ido kan makamai da kuma wuraren ajiyar makamai a wannan shiyya.

Taron na kwanaki uku zai taimaka wa mahalartan da suka fito daga kasashe goma sha biyar na gamayyar kungiyar ECOWAS na yin musanyar "halayya mai kyau" da aka samu a cikin tsarin shirin da aka gudanar a kasar Cote d'Ivoire, tare da tallafin kudin kasar Jamus.

A lokacin bikin bude taron, mista Coulibaly Kani-Diabate na kasar Mali, ya bayyana cewa, fataucin makamai na kasancewa matsala a nahiyar Afrika, shi ma ya nuna fatan cewa, wannan taro zai taimaka wajen daidaita ayyuka domin ko wace kasa ba za ta iya warware matsalar tsaro a gaban wasu sabbin barazana ba, musamman ma ta'addanci.

Shugaban kwamitin yaki da yaduwar kananan makamai (ComNat-ALPC) na Cote d'Ivoire, Kouadio Yao, ya kara jaddada kan yanayin da duniya take ciki na fama da sabbin barazana ta fuskar tsaron kasa da kasa.

A kasar Cote d'Ivoire, shirin da kwamitin ComNat-ALPC ya gudanar tare da taimakon kasar Jamus ya fara a shekarar 2012, kuma ya mai da hankali kan fannonin kula da ajiyar makamai da harsasai, da karfafa tsarin matakai da dokaki kan kananan makamai, da karfafa karfin jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro, daidaitawa, da hada kai, bincike da neman ci gaba.

Tun daga watan Nuwamban shekarar 2011, bayan fita daga ricikin bayan zabe a Cote d'Ivoire, kwamitin ComNat-ALPC na gudanar da ayyukan karbe makamai daga hannun jama'a. Fiye da makamai 9.661 aka karbe daga hannun fararen hula 4.158 da suka fito daga al'ummomi daban daban. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China