in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire za ta gudanar da zaben 'yan majalisu a ranar 20 ga Nuwamba
2016-05-06 09:53:31 cri

Mataimakin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Cote d'Ivoire CEI Gervais Coulibaly ya ce, ana sa ran hukumar za ta gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar nan da muke ciki.

Coulibaly wanda ya bayyana hakan ta wani shirin gidan rediyo, ya ce, hukumar ta CEI ta amince da gudanar da zaben majalisar dokokin kasar ne zuwa karshen shekarar nan, domin yin biyayya ga dokar kasa.

Hukumar CEI za ta gudanar da aikin sabunta rajistar masu kada kuri'a a karshen watan Mayu, kuma za ta tura tawagogin jami'anta kimanin 1,000 domin gudanar da aikin cikin nasara.

A shekarar 2015, yawan masu kada kuri'ar dake hannun hukumar ya kai mutane miliyan 6 da dubu 300.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China