in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsagerun Niger Delta sun sake fasa bututun mai a kudancin Najeriya
2016-05-27 09:59:15 cri

Sabuwar kungiyar tsagerun Niger Delta dake kudancin Najeriya, ta dau alhakin fasa wani bututun mai mallakar kamfanin hakar mai na Chevron a jihar Delta.

Kungiyar ta "Niger Delta Avenger" wadda a baya bayan nan ke ci gaba da barnata kayayyakin kamfanonin dake aikin hakar mai a yankin na Niger Delta, ta ce, ita ce ta tarwatse wani babban tankin kamfanin na Chevron dake Escravos, kusa da na'urorin dake samarwa kamfanin lantarki.

Hakan dai ya auku ne yayin da ma'aikatan kamfanin na Chevron ke kokarin gudanar da wasu gyare gyare ga bututan su da aka lalata a 'yan kwanakin da suka gabata. Sai dai ya zuwa yanzu kamfanin bai fidda wata sanarwa game da harin na ranar Alhamis ba.

Tuni dai kungiyar ta Avengers, ta umarci kamfanonin dake hakar mai a yankin da su fice kafin karshen watan nan. Kungiyar ta ce, tana daukar wadannan matakai na kaddamar da hare hare ne domin tirsasawa gwamnati magance matsalolin dake addabar yankin na su mai arzikin mai.

Manyan matsalolin na su dai a cewar su sun hada da karancin amfana daga albarkatun da ake fitar wa daga yankin na su, da gurbatar muhalli, kana suna da bukacin samar da dama ta cin gashin kan yankin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China