in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na shirin kawo karshen shigo da fetur daga ketare
2016-05-24 09:07:33 cri

Karamin ministan albarkatun man fetur a tarayyar Najeriya Ibe Kachikwu, ya ce, nan da shekara ta 2019, Najeriyar na fatan daina shigo da tacaccen man fetur daga ketare. Mr. Kachikwu wanda ya bayyana hakan yayin da yake bayani gaban wakilan jam'iyyun gama kai na kasar a birnin Ikkon jihar Legas, ya kara da cewa, ma'aikatar sa za ta kara yawan man da take hakowa a kullum, daga ganga miliyan 2.2 zuwa ganga miliyan 2.6 cikin 'yan shekaru masu zuwa.

Game da janye tallafin mai kuwa, ministan ya ce, daukar wannan mataki ya zama wajibi, duba da yadda harkar ke haifarwa kasar asarar dumbin kudade ta hanyoyar wakaci-ka tashi, da wasu masu ruwa da tsaki ke aikatawa a fannin. Don haka, a cewar sa, janye tallafin zai bude kofa ga dukkanin masu sha'awar shiga wannan kasuwa, wanda kuma hakan ne kadai zai kawo raguwar farashin na mai, nan da 'yan watanni masu zuwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China