in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwadibuwa ta bukaci kasashen yammacin Afirka su hadu don yakar ta'addanci
2016-03-16 09:46:15 cri

Shugaban kasar Kwadibuwa Alassane Ouattara ya bukaci sauran kasashe dake yammcin Afrika da su hada kai gu daya domin yakar ta'addanci.

Ouattara wanda yake magana ta kafar talabijin din kasar, ya bayyana kudurin kasar shi na aiki tare da sauran kasashen duniya domin kawo karshen ta'addanci.

Ya ce, za'a karfafa hadin gwiwwa da sauran kasashen da ke cikin yankin, da ma sauran kasashen duniya domin a taru a yaki ta'addanci.

Daga nan sai ya bukaci sauran kasashe da kada su tsorata, yana mai lura da su cewa, ta'addancin abu ne da za'a yaka ba tare da tausayawa ba.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka kai harin ta'addanci a wassu otel har uku a kasar wanda yawanci 'yan kasashen Turai ke sauka a ciki a Grand Bassam, harin da ya hallaka mutane a kalla 18, kungiyar al-Qaida reshen Maghreb ta dauki alhakin aiwatarwa.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China