A dunkule mutane 1275 da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su ne sojojin Najeriya suka ceto a yayin wani samamen hadin gwiwa tsakanin dakarun Najeriya da na kasar Kamaru.
Kakakin rundunar sojojin Najeriya, kanal Sani Usman, ya bayyana cewa, wadannan mutane da aka ceto suna can yanzu haka suna karbar jinya da binciken lafiyarsu daga hannun sojojin kafin a kwashe su zuwa sansanonin 'yan gudun hijira dake jihar Borno. A yayin wannan samame, aka lalata wuraren fakewa fiye da goma da ake zargin na 'yan ta'adda ne, kana kuma aka kashe wasu manyan kusoshin kungiyar Boko Haram uku da 'yan ta'adda 22. (Maman Ada)