in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure kimanin 700 ne suka mutu a makon da ya gabata a Bahar Rum
2016-05-30 10:30:39 cri
Wani jami'in hukumar kula da batun 'yan gudun hijira ta M.D.D. wato UNHCR a takaice ya furta a jiya Lahadi cewa, a cikin makon da ya gabata, wasu jiragen ruwa 3 sun nutse a tekun Bahur Rum, inda aka yi hasashe cewa, 'yan gudun hijira da bakin haure ba bisa doka ba kimanin 700 sun mutu.

Kakakin ofishin hukumar UNHCR da ke birnin Rome, Carlotta Sami ya bayyana a jiya cewa, a ranar 25 ga wata, 'yan gudun hijira kimanin 100 ne suka mutu sakamkon nutsewar jirgin ruwan dake dauke da bakin haure. A ranar 26 ga wata, wani jirgin na daban ya sake nutsuwa, wadanda suka tsallake rijiya da baya, sun bayyana cewa, akwai kimanin mutane 670 a cikin jirgin, koda ya ke an nasarar ceton mutane 104, kana an gano gawawwakin mutane 15, amma ya zuwa yanzu, mutane 550 sun bace. A ranar 27 ga wata, wani jirgin ruwa ya nutse, kuma an tabbatar da cewa, mutane 45 sun mutu, sai dai ba a tabbatar da yawan mutanen da suka bace ba.

Alkaluman da hukumar UNHCR ya bayar, ya nuna cewa, daga watan Janairu na bana zuwa yanzu, 'yan gudun hijira sama da 1500 sun mutu ko sun bace, yayin da suke kokarin shiga kasashen Turai ta tekun Bahar Rum. Bayan da yanayi a Bahar Rum ya kyautatu, an kara samun mafataucin jama'a zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya, inda ake kyautata zaton, kara samun mutanen da son shiga Turai ta barauniyar hanya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China