in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi maraba da sabbin likitocin kasar Sin da zasu ba da jinya a Senegal
2015-09-05 18:34:50 cri

A ranar Jumma'an nan aka shirya wata liyafa a ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Senegal, domin yin ban kwana ga likitocin kasar Sin rukuni na 15 da suka gama aikin ba da taimako a kasar, sannan aka marabci sabbin rukuni da suka isa kasar.

A cikin jawabinsa, Xia Huang, jadakan kasar Sin da ke Senegal ya ce, an yi imani da cewa, sabbin likitocin za su gaji kyawawan halaye da kuma ci gaba tare da dukufa tukuru kamar yadda sauran likitocin kasar Sin suka yi a baya. Ya kuma tabbatar da cewa za su hada kai da asitibin wurin, a kokarin ba da jinya ga mazauna kasar Senegal yadda ya kamata, lamarin da zai kara dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China