in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfafa dangantaka tsakanin Rasha da Sin muhimmin aikin diplomasiyya ne, in ji shugaba Putin
2014-05-19 10:22:01 cri

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha, ya ce, dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasarsa da Sin, ta kai wani muhimmin matsayi a tarihi, a kuma daidai gabar da sassan biyu ke daukar karin matakan habaka ta daga dukkanin fannonin ci gaba.

Shugaba Putin ya bayyana hakan ne ga 'yan jaridun kasar Sin, gabanin halartar sa babban taron tattaunawa kan inganta cudanya, da karfafa hadin gwiwar nahiyar Asiya na CICA, wanda zai gudana a birnin Shanghai a ranekun Talata da Laraba.

Shugaban kasar ta Rasha wanda kuma ke shirin gudanar da ziyarar aiki a nan kasar Sin bayan halartar wancan taro ya bayyana cewa, shi da shugaba Xi Jinping na nan kasar Sin, za su nazarci hanyoyin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka riga suka cimma, tare da fidda sabbin kudurorin da za su sanya gaba.

Daga nan sai ya bayyana hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, a matsayin sassan da ya dace kasashen biyu su kara azama a kan su.

A halin yanzu dai kasar Sin ce ke matsayi na daya, a fannin yawan kudaden cinikayya da Rasha, inda a bara jimillar kudaden cinikayyar dake tsakanin su ya tasamma dalar Amurka miliyan dubu 90. Yayin da kuma suke fatan daga wannan matsayi zuwa dala miliyan dubu 100 a badi, ya zuwa dala miliyan dubu 200 nan da shekarar 2020. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China