in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki 'dan adawar Nijar Hama Amadou da ake zargi da safarar jarirai
2016-03-30 10:31:30 cri

Tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Nijar, babban 'dan adawa Hama Amadou, da aka kama bisa zargin fataucin jarirai, ya samu sakin talala tun daga bakin ranar Talata, a cewar wani mataki na kotun birnin Yamai.

Wannan mataki ya zo bayan shigar da wata bukata ta lauyoyinsa domin neman wani sakin talala ga mutuminsu bisa dalilai na jin kai.

Dan takarar da ya sha kaye a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a fafatarsa tare da shugaba mai ci Issoufou Mahamadou, Hama Amadou an kwashe shi, a jajibirin zabe a cikin wani yanayi mai tada hankali, daga gidan kurkukun Filignue mai tazarar kilomita 180 daga arewacin birnin Yamai, zuwa birnin Paris na kasar Faransa bayan ya kwashe watanni hudu gidan yari.

Harkar fataucin jarirai ta shafi mutane kusan talatin, wadanda ya hada da Hama Amadou da matarsa, tsohon ministan kasa Abdou Labo da matarsa, Laftana kanal Oumarou Tawaye, da kuma wasu manyan mutanen kasar.

Dukkan wadannan mutane, baya ga Hama Amadou, dake gudun hijira a kasar Faransa, an tura keyar su gidan yari a Yamai da kuma kewaye, dalilin wannan harka, tun cikin watan Yunin da ya gabata, kafin su samu sakin talala.

Hama Amadu da ya gudu a kasar Faransa a cikin watan Agusta, an kama shi tun bayan ya dawo Nijar a ranar 14 ga watan Nuwamban da ya gabata, kuma aka tusa keyarsa gidan yarin Filignue.

Babban mai adawa da shugaba Mahamdou Issoufou, Hama Amadou, ya ci gaba da bayyana cewa, tuhumar da aka masa wani bita da kullin siyasa ne, masu mulki, a cewarsa, suka neman kaurace shi daga zaban shugaban kasa na shekarar 2016.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China