in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga matakin karshe na yaki da Boko Haram a Najeriya
2016-02-26 09:04:19 cri

Babban hafsan rundunar sojojin kasa ta Najeriya laftanal Janar Tukur Burutai, ya ce, yanzu haka dakarun sojin kasar na gaf da kakkabe burbishin mayakan Boko Haram dake yankunan kasar, kafin kuma a kai ga ceto 'yan matan nan na Chibok da ke tsare a hannun mayakan.

Burutai wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, yayin wata ganawa da ya yi da majalissar dattawan jihar, ya kara da cewa, matakan da ake dauka a yanzu, za su ba da damar kubutar da daukacin fararen hula da 'yan Boko Haram ke garkuwa da su.

Ya ce, rundunar sojin kasar za ta ci gaba da hadin gwiwa da kungiyoyin al'umma, domin tabbatar da baiwa wadanda suka rasa matsugunnan su kariya, tare da tallafawa wajen sake farfado da yanayin zaman lafiya da lumana a yankunan da rikici ya daidaita.

Har wa yau Burutai ya bayyana wa dattawan cewa, a baya bayan nan, an shawo kan matsaloli da dama, wadanda rundunar sojin ta sha fama da su a yakin da take yi da Boko Haram. Daga nan sai ya jinjina wa majalissar dattawan jihar bisa irin goyon baya da suke bayarwa, yana mai kira gare su, da ma daukacin al'ummar jihar da su kara hakuri, musamman game da matakan da ake dauka, har a kai ga cimma nasarar da aka sanya gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China