Kafin haka Sergei Lavrov, ya bayyana ma 'yan jarida na kasashen Sin da Japan da Mongolia cewa, ya kamata dukkan kasashen da batun tekun Nanhai ya shafa, su bi hanyar diplomasiyya don warware batun. Sannan yayi gargadin cewa, ya zama wajibi ga kasashen da ba su da nasaba da batun kai tsaye, su dakatar da duk wane yunkurin tsoma baki kan wannan batu, ko kuma mayar da batun a matsayin batun siyasar duniya. (Zainab)