in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana fatan OPEC za ta takaita hako danyen mai
2016-04-20 10:08:43 cri

Gwamnatin Najeriya ta fada a Talatar da ta gabata cewa, tana da kyakkyawan fatan kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC za ta cimma yarjejeniya game da batun takaita hako danyen mai a nan gaba.

Ministan albarkatun man fetur na kasar Ibe Kachikwu shi ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a Lagos cewa, duk da rashin cimma matsayar da aka samu a yayin taron da aka gudanar a birnin Doha, kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da tuntubar juna domin samun maslaha ba.

Ya kara da cewar, kungiyar OPEC za ta yi aiki tukuru domin lalibo hanyar da za'a cimma matsaya ta karshe game da batun.

Ya ce, ana sa ran idan komai ya daidaita, za'a kawo karshen faduwar farashin man a kasuwannin duniya, kuma za'a gudanar da taron ministocin mai na mambobin kasashen OPEC a watan Yuni a birnin Vienna na kasar Austria.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China