in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Zambia ta fara tsare-tsaren babban zaben kasar
2014-11-04 09:52:03 cri

Shugabar hukumar gudanar da zabe ta kasar Zambia Ireen Mambilima ta ce, tuni hukumarta ta fara tsara yadda zaben shugaban kasar zai wakana biyowa bayan rasuwar shugaba Michael Sata.

Uwargida Mambilima, wadda ta bayyana hakan yayin zantawar ta da 'yan jaridu ta ce, hukumar ta ECZ za ta kara azama a shirye-shiryen da take yi bayan bikin binne gawar shugaban kasar, ko da yake dai ba ta bayyana yawan kudin da zaben dai lakume ba.

Tuni dai wasu daga al'ummar kasar suka fara bayyana shawarar baiwa mataimakin shugaba Sata Guy Scott, damar ci gaba da jagorancin kasar ya zuwa shekarar 2016, lokacin da wa'adin mulkin marigayin zai cika, sa'ar da kuma za a gudanar da babban zaben kasar.

Shi dai Guy Scott, 'dan shekaru 70, ba shi da hurumin tsayawa takarar shugaban cin kasar, kasancewar iyayensa ba haifaffun kasar ta Zambia ba ne.

Kafin rasuwarsa, shugaba Sata shi ne shugaban kasar na 5, kuma shugaban Zambia na 2 da ya rasu yana kan ragamar mulkin kasar, bayan shugaba Levy Mwanawasa wanda ya rasu cikin watan Agustan shekarar 2008. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China