in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagogin masu sa ido sun yaba yadda zaben shugaban Zambia ya gudana
2015-01-21 10:08:48 cri

Masu sa ido kan zaben shugaban kasar Zambia daga ciki da wajen kasar sun bayyana cewa, zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a dukkan rufunan zaben kasar duk da wasu 'yan matsaloli da ba za a rasa ba, kamar isar kayayyakin zaben a makare sakamakon rashin kyan yanayi.

Babban darektan kungiyar shirya zabubbuka (FODEP) Macdonald Chipenzi ya ce, kungiyarsa ta gamsu da yadda zaben ya gudana duk da wasu 'yan matsaloli da aka fuskanta a wasu cibiyoyin kada kuri'a. Suna masu fatan cewa, yanayin zai dore ko da bayan an fara fitar da sakamakon zaben.

Ita ma shugabar tawagar kasuwar bai daya ta kasashen dake gabashi da kudancin Afirka (COMESA) da ke sa ido kan zaben, jakada Simbi Veke Mubako ta yabawa hukumar zaben kasar Zambia (ECZ) kan yadda ta tafiyar zaben.

Bugu da kari, ita ma kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yabawa hukumar zaben kasar ta Zambia kan yadda zaben shugaban kasar ya gudana lami lafiya. A halin da ake ciki, shugabar hukumar zaben kasar ta Zambia Prissila Isaacs ta bayyana farin cikinta kan yadda zaben ya gudana cikin nasara duk da wasu 'yan matsaloli da aka fuskanta wajen raba kayayyakin zaben a wasu wurare.

Sai dai shugabar hukumar zaben ta karyata jita-jitar da shugaban 'yan adawa Hakainde Hichilema ke yayatawa cewa, wai hukumar ta jinkirta kai kayayyakin zaben zuwa yammaci da arewa maso yammacin kasar ce domin ta yi magudin da zai baiwa 'dan takarar gwamnati Edgar Lungu nasara.

Shi dai shugaban 'yan adawa Hichilema na jam'iyyar UPND, yana zargi cewa, hukumar zaben ta ki tura kayayyakin zaben ne domin tauye hakkin magoya bayansu na zaben 'dan takararsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China