in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Zambiya ya lashe zaben shugaban jam'iyyar PF
2014-12-01 10:23:24 cri

A ranar Lahadin nan ministan tsaron kasar Zambiya Edgar Lungu ya lashe zabe ba tare da hamayya ba na shugabancin babban jam'iyyar kasar mai mulki, lokacin taron jam'iyyar da aka yi a birnin Kabwe.

Lungu wanda ya zama 'dan takara mafi karbuwa cikin 'yan takara 9 da suka tsaya ya nuna sha'awarsa na maye gurbin marigayi shugaban kasar Michael Sata wanda shi ne shugaban jam'iyyar mai mulkin Patriotic Front wato PF. Wannan zaben ya ba Edgar Lungu matsayin zama 'dan takaran shugabancin kasar da za'a yi a watan Janairun mai kamawa bayan da sauran 'yan takaran guda 8 suka ki bayyana wajen zaben.

Bisa tsarin dokar jam'iyyar, wajibi ne 'dan takarar shugabancin jam'iyyar ya samu goyon baya daga a kalla masu goyon bayan 200 daga gundumomi 10 da ake da su a kasar.

Jami'in zabe Tutwa Ngulube shi ya sanar da sakamakon zaben da ya tabbatar da Edgar Lungu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar, wani yunkurin da ya janyo gaggarumin biki da farin ciki daga magoya bayansa a dandalin zaben na Mulungushi Rock of Authority.

Shugaban babban taron Inonge Wina, tuni ta sanar da kammala taron. Za'a gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 20 ga watan Janairu mai zuwa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China