in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
HCR ta kwashe 'yan gudun hijirar Somaliya fiye da 13,800 dake sansanin 'yan gudun hijira na Dadaad dake Kenya
2016-05-17 10:31:38 cri
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta MDD (HCR) ta bayyana cewa ta mayar zuwa kasarsu, tun daga ranar 28 ga watan Afrilu, 'yan gudun hijirar Somaliya kusan 13,800 dake sansanin 'yan gudun hijira na Dadaad dake kasar Kenya, bisa shirin kwashe 'yan gudun hijira zuwa kasarsu bisa yarda da aka fara a cikin watan Disamban shekarar 2014. A cewar wata sanarwar HCR da aka fitar a ranar Litinin, 'yan gudun hijirar Somaliya 7,703 ne aka kwashe su zuwa kasarsu tsakanin watan Janairu da Afrilun wannan shekara. Tun lokacin fara wannan aiki a cikin watan Disamban shekarar 2014, ayarin motoci 63 da na jiragen sama 75 aka shirya zuwa kasar Somaliya (ayari 67 zuwa birnin Mogadiscio, 4 zuwa Kismayo kana 4 zuwa Baidoa), in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China