Wani jami'in soja mai suna Abdullahi Macalli ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, dakarun hadin gwiwar ba su samu wata matsala wajen sake kwato kauyen ba. Ko da yake mahukuntan Somaliya sun bayyana cewa, an halaka sojojinsu guda 8 bayan da aka yi musu kwanton bauna, yayin da aka halaka mayakan Al-Shabaab 12.
Kwato kauyen na Runir-good ya kara adadin yawan kauyukan dake karkashin ikon gwamnati, sakamakon hare-haren hadin gwiwa da dakarun sassan biyu suka kaddamar.
A ranar Lahadi ne mayakan na Al-Shabaab suka sake kwato kauyen Runir-good, inda suka yi ikirarin halaka sojoji sama da 32, ciki har da wani babban jami'in soja a garin, kwana guda bayan da garin ya fada hannun sojoji gwamnati. (Ibrahim)