in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al-Shabaab ta sake amshe wani yanki da sojojin gwamnatin Somalia suka kwace
2016-05-02 12:17:13 cri
Kungiyar Al-Shabaab dake kasar Somaliya, ta sake amshe ikon yankin Runir-god mai nisan kilomita 180 a arewa da birnin Mogadishu, bayan wani dauki ba dadi da mayakan suka kwashe tsawon lokaci suna gwabzawa da dakarun gwamnatin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa garin wanda ke tsakiyar yankin Shabelle, ya sake komawa karkashin ikon mayakan na Al-shabaab a jiya Lahadi, bayan da suka samu nasara kan dakarun gwamnati, suka kuma hallaka sojoji 32 ciki hadda manyan hafsoshi.

Sai dai a cewar Janar Mohamed Mohamud Saney, na rundunar sojin gwamnatin kasar, kungiyar ta Al-shabaab ta kambama nasarar da take ikirarin samu. Amma duk da hakan Saney ya tabbatar da rasuwar sojojin gwamnati 8 yayin gumurzun da ya auku. Ya kuma ce an hallaka dakarun Al-Shabaab 12 yayin bata-kashin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China