Shugaba Omar Al-Bashir na Sudan zai iso nan birnin Beijing na kasar Sin a Litinin din nan, domin halartar bikin cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin jinin harin Japanawa, yayin wata ziyara ta kwanaki hudu da zai gudanar.
A cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan Ali Al-Saddiq, shugaba Al-Bashir zai gana da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, domin karfafa dangantakar sassan biyu, da kuma karfafa zumuncin dake tsakaninsu.
A daya hannun ministan ma'aikatar sufuri da ginin hanyoyi Makkawi Mohammed Ahmed, ya shaidawa manema labaru cewa, shugaban na Sudan, zai halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ginin wani sabon layin dogo wanda wani kamfanin kasar Sin zai gudanar a gabashin kasar Sudan.
Ahmed ya ce, bisa kiyasi, layin dogon mai tsahon kilomita 1,000 zai lashe kudi har dalar Amurka biliyan 1 da miliyan dari hudu. Kaza lika shugaba Al-Bashir zai shaida sanya hannu kan kwangilar sayen wasu jiragen sama 2, da jiragen ruwa 9, da kuma hayar wasu jiragen sama mallakar kasar Sin guda uku. (Saminu)