in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a gina makarantar dinke abokantakar Sin da Sudan a Omdurman dake Sudan
2014-05-14 11:03:47 cri

A halin da ake ciki, ma'aikatar ilmi ta kasar Sudan dake Khartoum da kuma asusun kasar Sin na samar da zaman lafiya da raya kasa sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya ta kafa wata makaranta a garin Omdurman, domin dinke abokantakar kasar Sin da Sudan, wannan yarjejeniya ta biyo bayan wata ambaliyar ruwan da aka yi kwanan nan, wacce ta abkawa jihar kuma ta yi sanadiyyar lalacewar makarantu masu yawa.

A yayin da yake jawabi a wurin taron kaddamar da ginin, karamin ministan ababen more rayuwa da sufuri, Hammad Qassim ya ce, jama'ar kasar Sin ne suka kirkiro da aikin na gina makarantar a karkashin asusun samar da zaman lafiya da raya kasa na kasar Sin, a sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a kwanan baya, wadda ta abkawa a kasar Sudan, kuma ta yi sanadiyyar lalata makarantu da dama.

Ministan ya ce, kudin gina makarantar ya kai kimanin dalar Amurka dubu 500, kamar yadda ya ce, za'a fara aiwatar da ginin nan take.

Mataimakin babban sakatare na asusun samar da zaman lafiya da raya kasa na kasar Sin Ji Ping ya ce, ambaliyar ruwan ta lalata makarantu da yawa a Sudan, kuma Sudan tana fatan kasar Sin za ta gina wasu makarantu a kasar, shi ya sa muna kokarin gina wannan makarantar a Omdurman. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China