Ministan ma'aikatar hanyoyi da gadoji na kasar Sudan Abdul-Wahid Yousif, ya ce, hadin gwiwar kasar sa da kasar Sin, na taimakawa aikin da ake yi na ginin sabuwar hanyar mota wadda za ta hada yankunan Afirka da dama.
Yousif wanda ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Sin, ya kara da cewa, baya ga yankunan Darfur, da Kordofan, da birnin Khartum da hanyar za ta ratsa, za kuma ta hade Sudan da wasu manyan yankunan kasashen yammacin Afirka, ciki hadda Kamaru, da Najeriya, da Chadi da kuma janhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Tun cikin shekarar 1954 ne dai aka fara tunanin gina wannan hanya, amma tarin matsalolin kudi da na tsaro suka hana aiwatar da hakan. Amma a cewar Yousif, yanzu haka an kai ga kammala kaso 60 bisa dari na aikin wannan hanya mai tsahon kilomita 1200. (Saminu)