in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da WIPO sun amince da jarjejeniyar karfafa hadin gwiwa a fannin kare fasaha
2016-05-12 10:05:22 cri

Kasar Sin da kungiyar dake kare ikon mallakar fasaha ta kasashen duniya ko WIPO a takaice, sun rattaba hannu kan jarjejeniyar karfafa hadin gwiwa a fannin ikon kare mallakar fasaha.

Ministan masana'antu da cinikayyar kasar Sin Zhang Mao, da babban daraktan WIPO Francis Gurry ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a madadin sassan biyu.

Yarjejeniyar dai ta yi la'akari da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki, da ka'idodin gyare gyare ga harkokin cinikayya, da na mallakar lambobin shaidar fasaha. Kaza lika yarjejeniyar ta lura da rawar da kasar Sin ke takawa ga ikon mallakar fasaha a duniya.

A bara alkaluma sun nuna cewa, a nan kasar Sin, masu bukatar lambobin shaidar mallakar fasaha kimanin miliyan 2.9 ne suka mika takardun su na neman izini, adadin da ya zarta 766,319 da aka samu a shekara 2006.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, a bara kasar Sin ce ta 6 a jerin kasashen da suka fi mika bukatar neman wannan lambobi, karkashin tsarin Madrid, cikin jimillar wannan adadi 2,321 sun fito ne daga kasar Sin.

Mr. Zhang Mao ya bayyana tasirin yayata lambobin mallakar fasaha na kasar Sin, bisa matsayin kasar ta biyu a duniya a fannin ci gaban tattalin arziki.

Ministan ya ce, Sin za ta ci gaba da gudanar da gyaran fuska, da baiwa masu lambobin mallakar fasaha dama ta gogayya da juna, da bunkasa kere-kere domin wanzar da ci gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China