Kamfanin dake kula da albarkatun man fetur na Najeriya ya fada a Talatar da ta gabata cewar, ya tanadi matakai da suka dace domin kawo karshen karancin man fetur da ya jima yana addabar kasar.
A cikin wata sanarwa, kamfanin na NNPC ya ce, matsalar karancin man fetur a kasar ba ta da alaka da biyan kudaden ariya na tallafi ga dillalan fetur na kasar, sai dai ya shafi hanyoyin rarraba man zuwa sassan kasar.
NNPC ya bai wa al'ummar kasar tabbaci game da daukar kwararan matakai na shawo kan matsalar nan da kwanaki kadan masu zuwa.
Kamfanin man ya kara da cewar, a halin da ake ciki yanzu, an samu gagarumar nasara game da batun samar da man fetur, da kuma rarraba shi ga dukkanin jihohin kasar, sannan ya ba da tabbacin samun wadataccen man a kasar baki daya.
Bugu da kari, kamfanin ya ce, zai sa ido sosai domin tabbatar da ganin ana bin ka'idoji game da kayyadadden farashi da hukuma ta amince da shi, sannan za'a ladaftar da dukkan gidajen man dake sayar da man sabanin farashin da aka kayyade, ko kuma masu boye man za su gamu da fushin hukuma, kuma za a hukunce su bisa ka'ida.(Ahmed Fagam)