Ministan ma'aikatar kudin kasar Ghana Seth Terkper, ya ce, a bara kasarsa ta fidda danyen mai da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 978.8 daga mahakar man kasar ta Jubilee.
Mr. Terkper wanda ya bayyana hakan cikin wata wasika da ya aike ga taron masu ruwa da tsaki kan harkokin hakar ma'adanai a kasar, ya kara da cewa, mahakar ta samar da danyan mai har ganga miliyan 37.2 a shekarar ta 2014, adadin da ya haura na shekarar 2011 da kaso 42.6 bisa dari.
A cewarsa, Ghana ta samu damar fara hako mai daga Jubilee ne a watanni 3 na farkon shekarar bara, bayan da bankin samar da ci gaba na kasar Sin CDB, ya samar da kudaden sarrafa iskar gas a Atuabo.
Duk dai da ci gaban da kasar ta samu a wannan fanni, Mr. Terkper ya ce, faduwar da farashin mai ke yi yanzu haka a kasuwannin duniya, na tattare da kalubale da kuma wasu damammaki ga kasar ta Ghana.
Ministan kudin kasar ta Ghana ya ce, karyewar farashin man zai baiwa Ghana damar rage kudaden da take kashewa, wajen shigo da mai daga ketare, yayin da a hannu guda gwamnati za ta rasa wani bangare na kudaden shigar da take samu daga ribar fidda nata man sakamakon faduwar farashin. (Saminu)