Ma'aikatan mai a Najeriya sun kaddamar da zanga-zanagr gama gari a ranar Laraban nan, abin da ya dakatar da ayyukan matatar man kasar ta NNPC, bayan da gwamnati ta sanar da kasa kamfanin zuwa rukuni 7 a ranar Talatan makon nan.
Karamin ministan mai kuma shugaban kamfanin mai na kasar wato NNPC ya ce, an dauki wannan mataki ne bayan ganawa da manyan kamfanonin mai.
Sai dai kuma zanga zangar gama gari karkashin jagorancin kungiyar ma'aikatan ta NUPENG da kuma PENGASSAN sun bayyana fusatar su a kan hakan.
Kungiyoyin sun zargi gwamnati da kin jawo masu ruwa da tsaki a cikin shawarar da suka yanke, abin da ya sa suka bukaci a yi watsi da shi.(Fatimah)