Tawagar jami'an aikin wanzar da zaman lafiya ta MDD a Cote d'ivoire UNOCI ta ce, an gudanar da zaben shugaban kasar a ranar Lahadin da ta gabata ba tare da tashin hankali ba.
Yan takara 10 ne suka tsaya a zaben, ciki har da shugaban kasar mai ci Alassane Ouattara, kuma ana sa ran zaben zai kawo karshen tashin hankalin da ya gurgunta kasar sakamakon rikicin bayan zabe da ya barke a kasar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011 bayan zaben shugaban kasar a wancan lokaci.
Mai magana da yawun babban sakataren MDD Stephane Dujarric, ya ce, ana sa ran bayyana alkaluman farko na sakamkon zabe a yau ko gobe Laraba.
Dujarric ya ce, jami'an UNOCI suna taimakawa jami'an 'yan sandar kasar da sojoji da sauran jami'an tsaro a kasar domin tabbatar da tsaro a kasar.
Ya ce, MDD ta tanadi jiragen sama na ko ta kwana da sauran ababan sufuri domin jigilar muhimman kayyakin zaben zuwa birnin Abidjan.(Ahmad Fagam)