in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana zaben Cote d'Ivoire zai kawo karshen ricikin kasar
2015-11-03 09:53:46 cri

A ranar Litinin din nan, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya taya Alassane Ouattara murnar lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu, inda ya bayyana yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da cewar wata alama ce dake nuna zaman lafiya zai wanzu a kasar.

Da yake yin lale marhabun da sakamakon karshe na zaben, Ban, ya taya gwamnati da al'ummar kasar Cote d'Ivoire murnar kammala zaben cikin kwanciyar hankali.

An gudanar da zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire ne a ranar 25 ga watan Oktoba da ya gabata, kuma 'yan takara 10 ne suka fafata a zaben, ciki har da Mista Oattara, shugaban kasar mai ci a halin yanzu.

MDD ta yaba wa hukumar zaben kasar bisa yadda ta jagoranci gudanar da zaben cikin hikima da basira, da kuma bin dokokin kundin tsarin mulkin kasar wajen shiryawa da aiwatar da zaben.

Zaben na ranar 25 ga watan Oktoba, ya kasance tamkar ma'auni ne da zai tabbatar da makomar kasar, bayan tashin hankalin da kasar ta tsunduma bayan zaben shugaban kasar a shekarar 2010 zuwa 2011, lamarin da ya jefa kasar cikin rikici, wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da dubu 3 a kasar.

Sanarwar ta kara da cewar, MDD za ta ci gaba da yin aiki tare da Mista Ouattara da kuma al'ummar kasar ta Cote d'Ivoire domin tabbatar da samun dauwamamman zaman lafiya a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China