in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da kammala zagayen farko na babban zaben Kwadibuwa
2015-10-28 10:19:01 cri

Magatakardan MDD Ban Ki-moon a ranar Talatan nan ya yi maraba da kammala zagaye na farko na babban zaben kasar Kwadibuwa lami lafiya a ranar Lahadi.

Mr Ban, a cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar, ya ce, a lokacin da ake jiran sakamakon zaben karshe, akwai bukatar dukkanin shugabannin siyasar kasar da masu ruwa da tsaki da su kauce wa duk wasu kalamai da za su iya tunzura tashin hankali.

Ya kuma jaddada cewa, kiran shi a kan masu ruwa da tsaka na kasar da su warware kowane rashin fahimta da ka iya bullowa a tsakanin su ta hanyar bin tsarin shari'a yadda ya kamata.

Yawan al'ummar kasar Kwadibuwa miliyan 6.3 ne ake sa ran za su jefa kuri'unsu a rumfunar zabe 19,841 a duk fadin kasar, da ma kasashen waje.

Zaben na ranar 25 ga watan Oktoba ana mashi kallon mai muhimmanci wajen samar da dawamammen zaman lafiya bayan tashin hankalin da ya biyo bayan babban zaben shekara ta 2010 da 2011 wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka fiye da 3,000 a tsawon makonni biyu da aka yi ana tashin hankali tsakanin magoya bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo da zababben shugaba Alassane Ouatarra.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China