IMF: saurin karuwar tattalin arzikin kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara zai ci gaba da raguwa a shekarar 2016
Asusan bada lamuni na IMF a yau Laraba ya fidda wani hasashe kan makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika dake kudu da Sahara, inda asusun ya ce sakamakon wasu dalilai da suka hada da raguwar farashin kayayyakin da ake bukatar da yawansu, da bala'in fari, da kuma tasirin da Ebola ta haddasa da dai sauransu, yawan karuwar tattalin arziki a kasashen dake kudancin Sahara zai yi kasa zuwa kashi 3 cikin dari kacal a shekarar 2016, adadin da zai zamo mafi kankanta tun bayan shekarar 1999. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku