in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da Sin za su karfafa huldar dangantaka
2016-05-04 10:38:49 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) da kasar Sin sun lashi takobin karfafa huldar dangantaka a fannoni da dama domin samun kyakkyawar fahimta tsakanin Sin da kasashen Afrika.

Wannan yunkuri ya zo ne a lokacin bikin murnar cika shekara guda daya ta kafa tawagar jakadun kasar Sin a AU wanda ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar AU, da sauran manyan jami'an na AU, da jami'an diplomasiyya dake zaune a Addis Ababa, da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa da na kamfanonin kasar Sin ne suka halarci bikin, inda wasu kwararrun mawaka na kasar Sin suka shirya wasannin masu nishadantarwa a lokacin biki.

Da yake tsokaci a yayin taron, Kuang Weilin, shugaban tawagar jakadun kasar Sin a kungiyar AU, ya ce, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar AU tana kara samun bunkasuwa daga dukkan fannioni.

Ya ce, an samu gagarumin ci gaba game da hadin kan dake tsakanin bangarorin biyu ta fuskar cinikayya, da hadin kai, da zaman lafiya da samar da tsaro a tsakanin Sin da kungiyar AU.

Kuang Weilin ya ce, a lokacin taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afrika wato (FOCAC) wanda aka gudanar a watan Disambar bara a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ambata muhimman bangarori 10 na hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, inda kasar Sin ta yi alkawarin samar da kudi dalar Amurka biliyan 60 domin aiwatar da shirin shekaru 3.

Jakadan na Sin ya fada cewar, taron na FOCAC tamkar daura damba ne a tsarin jadawalin dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika na tsawon lokci, kuma kasar Sin za ta ci gaba da yin aikin tare da kasashen Afrikan domin aiwatar da shirye shiryen da aka cimma a lokacin taron.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China