in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bude ofishin wakilci a helkwatar AU
2015-05-08 09:42:57 cri

A jiya Alhamis ne aka gudanar da bikin bude sabon ofishin wakilcin kasar Sin, a helkwatar kungiyar tarayyar Afirka dake birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Hakan kuwa ya biyo bayan aniyar kasar ta Sin, game da karfafa dangantakar kawance tsakaninta da daukacin kasashen nahiyar Afirka. Matakin da kuma ya sanya kasar kasancewa ta farko, da ta kafa ofishin wakilci a hukumar gudanarwar kungiyar ta AU.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming, da kuma shugabar hukumar gudanarwa ta kungiyar AU uwar gida Nkosazana Dlamini Zuma ne suka jagoranci bude ofishin, wanda kwararren jami'in diplomasiyyar kasar Sin Kuang Weilin zai jagoranta.

Ofishin dai na da sassan siyasa, da na tattalin arziki, da al'adu, wanzar da zaman lafiya da kuma sashen tsaro. An kuma fatan ayyukansa za su ba da damar gudanar da karin musaya, da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Kaza lika ana sa ran ofishin zai taimaka wajen daga matsayin dangantakar sassan biyu zuwa wani sabon matsayi.

Da take tsokaci jim kadan bayan bude wannan ofishin, uwar gida Zuma ta taya kasar Sin murna, tana mai cewa, daukacin wakilan nahiyar Afirka dake AU na kallon wannan mataki, a matsayin wata gudamma ta kasar Sin ga ci gaban nahiyar Afirka baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China