in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da Sin sun amince da yarjejeniyar hadin gwiwar bunkasa ababen more rayuwa
2015-01-28 10:36:50 cri

Wakilan kasar Sin da na kungiyar hadin kan Afirka ta AU, sun rattaba hannun kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa game da bunkasa masana'antu, da samar da ababen more rayuwa a nahiyar Afirka.

Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar AU uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming ne suka sanya hannu, kan takardun yarjejeniyar a madadin bangarorin biyu, a helkwatar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Rahotanni na cewa, manufar hakan ita ce fidda tsare-tsare, na samarwa kasashen Afirka manyan hanyoyin mota da za su hade sassan nahiyar, da bunkasa sufurin jiragen kasa da na sama, da kuma habaka masana'antu.

Yarjejeniyar ta kasance daya daga muradun dinke nahiyar Afirka, da kungiyar ta AU ta sanya a gaba nan da shekarar 2063.

Wannan mataki dai na zuwa ne gabanin taron AU karo na 24 da za a bude a ranar Juma'a, wanda zai kunshi wakilan kwamitin din din din na kungiyar ko PRC a takaice.

Da take tsokaci game da hakan, uwargida Zuma ta ce, Sin da Afirka sun dade suna gudanar da hadin gwiwa, da tallafawa juna a fannoni daban daban.

A nasa bangare, Mr. Zhang cewa ya yi, yarjejeniyar ta kunshi manyan ayyuka da dama, wadanda za a iya cimma nasarar aiwatar da su idan har an sanya himmar da ta kamata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China