in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da fadada hadin gwiwa da AU, in ji Yang Jiechi
2015-02-10 10:06:42 cri

Mamba a majalissar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, ya ce, kasarsa za ta ci gaba da zurfafa kawancen dake tsakaninta da kungiyar hadin kan Afirka AU.

Mr. Yang ya bayyana hakan ne ga manema labarai, bayan wata ganawa da ya yi da shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe a jiya Litinin.

Ya ce, hakan zai baiwa sassan biyu cikakkiyar damar cimma moriyar juna a fannonin tattalin arziki da na zamantakewa.

Da yake tsokaci game da alakar dake akwai tsakanin Sin da nahiyar Afirka, Yang Jiechi ya ce, martaba juna, da aiwatar da manufofin bunkasuwa tare, da amincin dake tsakanin sassan biyu, alamu ne dake nuni ga irin kyakkyawar alakar dake tsakanin su.

Kaza lika Mr. Yang ya bayyana irin kulawa da kasar Sin ke nunawa ga ci gaban nahiyar Afirka, ciki hadda batun cimma nasarar kudurin ci gaban nahiyar nan da shekaru 50 masu zuwa, wanda aka yiwa lakabi da muradun ci gaba na shekarar 2063. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China