in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An daddale yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci a tsakanin Sin da Australia
2015-06-17 11:31:19 cri

A yau ne ministan kasuwancin kasar Sin Gao Hucheng da ministan cinikayya da zuba jari na kasar Australia Andrew Rob suka daddale yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci a birnin Canberra, hedkwatar mulkin kasar Australia, a madadin gwamnatocin kasashen biyu. Kuma bikin ya samu halartar firaministan kasar Australia Tony Abbott.

Shirin daddale yarjejeniyar ya aza wani harsashi ga jerin ayyukan neman samun izni daga gwamnatocin kasashen biyu da za a gudanar, a kokarin kaddamar da shirin yarjejeniyar cikin hanzari

Wannan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci a tsakanin Sin da Austalia ta shafi fannoni fiye da goma, wadda ta kasance daya daga cikin yarjeniyoyi mafi muhimmanci da kasar Sin ta rattaba hannu a kai tare da wasu kasashen duniya wajen yin cinikayya da zuba jari ba tare da wani shinge ba.

Bisa abubuwan da aka tanada a cikin yarjejeniyar, za a soke harajin kwastam da ake biya ga kayayyakin shigi da fice, wadanda darajarsu ta kai kashi 85.4 cikin dari bisa dukkan jimillar kudin cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

Bugu da kari, a fannin zuba jari, bangarorin biyu za su rika yiwa juna rangwame. Sa'anan nan, kasar Australia za ta rage sharuddan da ta sanya game da adadin kamfanonin kasar Sin a bangaren zuba jari a kasar, baya ga saukaka musu a wannan fanni. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China