in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na damuwa kan halin tarbarewar matsalar tsaro a kasar Somaliya
2016-04-23 11:47:33 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana damuwarsa game da halin tabarbarewar matsalar tsaro a kasar Somaliya, duk da kuma nuna gamsuwarsa da ci gaban da aka samu ta fuskar siyasa a cikin wannan kasa a tsawon shekaru hudu da suka gabata.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis da yamma, mambobin kwamitin tsaro sun jaddada yin allawadai da hare hare da kuma shigar da yara kanana da kungiyar ta'addanci ta Al-Chabaab take yi tare da kuma jinjinawa tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake kasar Somliya (AMISOM) da rundunar sojojin kasar Somaliya game da kokarin rage barazanar da kungiyar ta Al-Chabaab.

Haka kuma mambobin kwamitin sun jaddada muhimmancin ci gaba da ayyukan kai samame na AMISOM da rundunar sojojin Somaliya kan mayakan Al-Chabab, bisa tsarin hada kai yadda ya kamata da kuma mutunta 'yancin jin kai na kasa da kasa da kare fararen hula. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China