in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka sun hallaka dakarun Al-Shabaab na Somaliya 12
2016-04-13 10:11:23 cri
Ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana a ranar 12 ga wata cewa, a wannan mako, sojojin Amurka sun kai hare-haren sama har sau 2 kan wani sansanin horo na kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya, inda suka hallaka mayakan kungiyar 12.

A gun taron manema labarun da aka yi a wannan rana, kakakin ma'aikatar tsaron Amurka Jeff Davis ya bayyana cewa, a daren ranar 11 ga wata, da safiyar ranar 12 ga wata, agogon kasar ta Somaliya, sojojin Amurka sun jefa boma-bomai kan sansanin horo na kungiyar Al-Shabaab da ke yankin kudancin kasar Somaliya. Bisa kwarya-kwaryar tantancewa da aka yi, an hallaka dakaru dauke da makamai 12.

Davis ya ce, dalilin da ya sa aka kai harin sama kan sansanin shi ne, bisa bayanan leken asiri da kasar ta samu, dakarun dauke da makamai na sansanin na kawo kalubale ga sojojin Amurka.

Kungiyar Al-Shabaab na da alaka sosai da kungiyar Al-Qaeda, a cikin 'yan shekarun nan, sun kai hare-hare sau da dama a kasar Somaliya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China